عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه ، قال: لما غَسَّل النبيَّ صلى الله عليه وسلم ذَهَبَ يَلْتَمِسُ منه ما يُلتمس مِن الميِّت، فلم يَجِدْه، فقال: «بأبي الطيِّب، طِبتَ حيًّا، وطِبتَ ميتًا».
[صحيح] - [رواه ابن ماجه]
المزيــد ...
Daga Aliyu Bn Abi Xalib -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, bai samu komai ba, sai ya ce: Fansarka da Mahaifina , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu"
[Ingantacce ne] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]
Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, na bunda yake futa daga jikinsa na futsari ko bayan gida ko mai kama da shi, bai samu komai ba, saboda ana iya samun wani abu saboda sakin da gavvai suka yi, sai Ali ya ce: Fansarka da Mahaifina ya Manzon Allah , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu