عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «لا يَقْتَسِمُ وَرَثَتي دينارًا ولا درهمًا، ما تَرَكْتُ بَعْدَ نَفَقَة نسائي، ومئونَة عامِلي فهو صَدَقة».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Ba'a rabawa Magadana ko dinare daya ko Dirhami abunda na bari bayan abincin Iyalina, da ladan Ma'aikata na to sauran Sadaka ne"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Wannan Hadisn yana nuna cewa Magadan Manzon Allah SAW ba zasu raba -bayan Mutuwarsa- wani dinare ko irhami daga Dukiyarsa ba; Saboda Shi SAW yana daga cikin Annabawa kuma Annabawa basa gadar da Zinare ko Dirhami; Saboda su basa basa tara Duniya, Kuma kaxai Saqonsu shi ne shiryar da Mutane, to idan aka samu Wata Dukiya bayan Mutuwarsa to abincin Matansa ne, haka kuma na Halifansa ne bayansa, ko kuma duk wanda yake jagorantar Musulmai bayansa, kuma duk abunda ya karu kan hakan to sadaka ne

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Kurdawa
Manufofin Fassarorin