عن عائشة رضي الله عنها ، قالت: «ما تَرَك رسولُ الله صلى الله عليه وسلم دينارًا، ولا درهمًا، ولا شاةً، ولا بَعِيرًا، ولا أَوْصى بشيء».
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda fa ita- ta ce: "Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba"
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- tana bada labarin cewa Manzon ALlah SAW bai bar komai ba bayan Mutuwarsa kaxan ne ko mai yawa, kuma bai bar Akuya ba, ko kuma Raquma ko wanin hakan na dangogin Dukiya, Kuma bai yi wasiyya da wani abu ba, tana nufin Wasiyyar Kuxi na Musamman; Saboda Mutum yana iya yin Wasiyya ne idan za'a gajr shi, kuma shi SAW bai bar komai na Gadon ba da za'a gada ballantana yayi wasiyya a cikinsa, Kuma Haqiqa Manzon Allah SAW yayi wasiyya da wasu abubuwan daban, daga cikinsu akwai kula da Sallah, da kuma futar da Yahudawa da nasara daga Jazirar Larabawa

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Kurdawa
Manufofin Fassarorin