عن عائشة رضي الله عنها ، أنَّ أبا بكر دَخَل على النبي صلى الله عليه وسلم بعد وفاته، فَوَضَع فَمَهُ بَيْن عيْنَيْه، ووَضَعَ يديْه على صُدْغَيه، وقال: «وَانَبِيَّاهُ، وَاخَليلاهُ، وَاصَفِيَّاهُ».
[حسن] - [رواه أحمد]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- ce: "Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, ya sanya Hannayensa akan Mukamukinsa, kuma ya ce: "Ya Annabi, ya Badadi, ya zababbe"
Hasan ne - Ahmad ne ya rawaito shi

Bayani

Abubakar ya shiga Wajen Manzon Allah SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa a tsakanin Idanuwan Manzon ALlah SAW sai ya Sunbanceshi, kuma ya sanya Hannayensa a kan Muqamiqan Manzon ALlah SAW, su ne gefen Fuska daga Ido zuwa Kunne, kuma ya ce: "Muna rashin Annabinsa, Muna Rashin Masoyinsa, Muna rashin Zavavvensa" ai cewa shi ya kasance -Allah ya yarda da shi- yana jin ciwon Mutuwar Manzon Allah SAW kuma yana siffanta shi da cewa shi ya kasance yana fifitashi kan komai har kansa, kuma wannan shi ake kira Alhini, kuma idan bai kasance a cikinsa akwai futo na futo da Musiba da kuma raki ba, kuma idan ba'a xaga Murya ba, Kamar yadda Mata suke yi da Ihu da Kururuwa, to Wacan ya Halatta, Kuma shi ne abunda Abubakar yayi -Allah ya yarda da shi

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Kurdawa
Manufofin Fassarorin