عَنْ أبي سَلَمَةَ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَنَّ جَابِرَ بْنَ عَبْدِ اللَّهِ الأَنْصَارِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: وَهُوَ يُحَدِّثُ عَنْ فَتْرَةِ الوَحْيِ، فَقَالَ فِي حَدِيثِهِ:
«بَيْنَا أَنَا أَمْشِي إِذْ سَمِعْتُ صَوْتًا مِنَ السَّمَاءِ، فَرَفَعْتُ بَصَرِي، فَإِذَا المَلَكُ الَّذِي جَاءَنِي بِحِرَاءٍ جَالِسٌ عَلَى كُرْسِيٍّ بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، فَرُعِبْتُ مِنْهُ، فَرَجَعْتُ فَقُلْتُ: زَمِّلُونِي، فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَعَالَى: {يَا أَيُّهَا المُدَّثِّرُ1 قُمْ فَأَنْذِرْ} [المدثر: 2] إِلَى قَوْلِهِ {وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ} [المدثر: 5]. فَحَمِيَ الوَحْيُ وَتَتَابَعَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4]
المزيــد ...
Daga Abu Salama Ibnu Abdurrahman cewa Jabir Ibnu Abdullahi al-Ansari - Allah Ya yarda da su - ya ce: Alhali shi yana bada labari game da lokacin wahayi, a cikin zancensa sai ya ce:
"Wata rana ina tafiya sai na ji wata ƙara daga sama, sai na ɗaga ido na, sai ga mala'ikan da ya zo mini a (kogon) Hira a zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, ai na ji tsoronsa, sai na dawo sai na ce: Ki lulluɓeni, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da {Ya kai mai lulluɓa1 Ka tashi ka yi gargaɗi}[alMuddasir: 2] zuwa faɗinSa: {Ka ƙauracewa gumaka} [al-Muddassir: 5]. Sai wahayi ya tsananta kuma ya bibiyi juna.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari alhali shi yana bada labari game da tsayawar wahayi da kuma dakatar da saukarsa a farkon manzancinsa: Wata rana ina tafiya a lungun Makka sai na ji wata ƙara daga sama sai na ɗaga idona, sai ga mala'ikan da ya zo mini a kogon Hira yana zaune akan kujera tsakanin sama da ƙasa, sai na tsorata na razana daga gare shi, sai na dawowa iyalina sai na ce: Ku lulluɓeni da tufafi. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da: {Ya kai mai lulluɓa} mai lulluɓa da tufansa, {Ka ta shi} da kira {Ka yi gargaɗi} ka gargaɗar da wanda bai yi imani da saƙonka ba. {Ubangijinka} Ubangijinka abin bauta {Ka girmama} ka gode maSa ka girmamaShi. {Tufafinka} tufafinka {Ka tsarkake} ka tsamosu daga najasa, {Gumaka} da bautar gumaka da mutun mutumi {To ka ƙaurace} ka bari, sai wahayi ya yi ƙarfi bayan haka ya yi yawa.