Karkasawa: Sirah da Tarihi . Tarihin Annabi . .
+ -

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنِينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْها أَنَّهَا قَالَتْ:
أَوَّلُ مَا بُدِئَ بِهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنَ الوَحْيِ الرُّؤْيَا الصَّالِحَةُ فِي النَّوْمِ، فَكَانَ لاَ يَرَى رُؤْيَا إِلَّا جَاءَتْ مِثْلَ فَلَقِ الصُّبْحِ، ثُمَّ حُبِّبَ إِلَيْهِ الخَلاَءُ، وَكَانَ يَخْلُو بِغَارِ حِرَاءٍ فَيَتَحَنَّثُ فِيهِ -وَهُوَ التَّعَبُّدُ- اللَّيَالِيَ ذَوَاتِ العَدَدِ قَبْلَ أَنْ يَنْزِعَ إِلَى أَهْلِهِ، وَيَتَزَوَّدُ لِذَلِكَ، ثُمَّ يَرْجِعُ إِلَى خَدِيجَةَ فَيَتَزَوَّدُ لِمِثْلِهَا، حَتَّى جَاءَهُ الحَقُّ وَهُوَ فِي غَارِ حِرَاءٍ، فَجَاءَهُ المَلَكُ فَقَالَ: اقْرَأْ، قَالَ: «مَا أَنَا بِقَارِئٍ» قَالَ: «فَأَخَذَنِي فَغَطَّنِي حَتَّى بَلَغَ مِنِّي الجَهْدَ ثُمَّ أَرْسَلَنِي، فَقَالَ: اقْرَأْ، قُلْتُ: مَا أَنَا بِقَارِئٍ، فَأَخَذَنِي فَغَطَّنِي الثَّانِيَةَ حَتَّى بَلَغَ مِنِّي الجَهْدَ ثُمَّ أَرْسَلَنِي، فَقَالَ: اقْرَأْ، فَقُلْتُ: مَا أَنَا بِقَارِئٍ، فَأَخَذَنِي فَغَطَّنِي الثَّالِثَةَ ثُمَّ أَرْسَلَنِي، فَقَالَ: {اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ خَلَقَ الإِنْسَانَ مِنْ عَلَقٍ اقْرَأْ وَرَبُّكَ الأَكْرَمُ}»، [العلق:1-3] فَرَجَعَ بِهَا رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَرْجُفُ فُؤَادُهُ، فَدَخَلَ عَلَى خَدِيجَةَ بِنْتِ خُوَيْلِدٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا، فَقَالَ: «زَمِّلُونِي، زَمِّلُونِي» فَزَمَّلُوهُ حَتَّى ذَهَبَ عَنْهُ الرَّوْعُ، فَقَالَ لِخَدِيجَةَ وَأَخْبَرَهَا الخَبَرَ: «لَقَدْ خَشِيتُ عَلَى نَفْسِي» فَقَالَتْ خَدِيجَةُ: كَلَّا وَاللَّهِ مَا يُخْزِيكَ اللَّهُ أَبَدًا، إِنَّكَ لَتَصِلُ الرَّحِمَ، وَتَحْمِلُ الكَلَّ، وَتَكْسِبُ المَعْدُومَ، وَتَقْرِي الضَّيْفَ، وَتُعِينُ عَلَى نَوَائِبِ الحَقِّ، فَانْطَلَقَتْ بِهِ خَدِيجَةُ حَتَّى أَتَتْ بِهِ وَرَقَةَ بْنَ نَوْفَلِ بْنِ أَسَدِ بْنِ عَبْدِ العُزَّى، ابْنَ عَمِّ خَدِيجَةَ، وَكَانَ امْرَأً تَنَصَّرَ فِي الجَاهِلِيَّةِ، وَكَانَ يَكْتُبُ الكِتَابَ العِبْرَانِيَّ، فَيَكْتُبُ مِنَ الإِنْجِيلِ بِالعِبْرَانِيَّةِ مَا شَاءَ اللَّهُ أَنْ يَكْتُبَ، وَكَانَ شَيْخًا كَبِيرًا قَدْ عَمِيَ، فَقَالَتْ لَهُ خَدِيجَةُ: يَا ابْنَ عَمِّ، اسْمَعْ مِنَ ابْنِ أَخِيكَ، فَقَالَ لَهُ وَرَقَةُ: يَا ابْنَ أَخِي، مَاذَا تَرَى؟ فَأَخْبَرَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَبَرَ مَا رَأَى، فَقَالَ لَهُ وَرَقَةُ: هَذَا النَّامُوسُ الَّذِي نَزَّلَ اللَّهُ عَلَى مُوسَى، يَا لَيْتَنِي فِيهَا جَذَعًا، لَيْتَنِي أَكُونُ حَيًّا إِذْ يُخْرِجُكَ قَوْمُكَ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَوَ مُخْرِجِيَّ هُمْ؟»، قَالَ: نَعَمْ، لَمْ يَأْتِ رَجُلٌ قَطُّ بِمِثْلِ مَا جِئْتَ بِهِ إِلَّا عُودِيَ، وَإِنْ يُدْرِكْنِي يَوْمُكَ أَنْصُرْكَ نَصْرًا مُؤَزَّرًا. ثُمَّ لَمْ يَنْشَبْ وَرَقَةُ أَنْ تُوُفِّيَ، وَفَتَرَ الوَحْيُ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce:
Farkon abinda aka fara wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne kyakkyawan mafarki a cikin barci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya zo masa kwatankwacin hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaici, ya kasance yana kaɗaita a kogon Hira, sai ya yi ibada a cikinsa - shi ne ibada - a wasu ƙididdigaggun darare kafin ya koma gurin iyalansa, kuma yana yin guziri saboda hakan, sannan ya koma ga Nana Khadija, sai ya yi guzuri na kwatankwacinsu (kwanukan), har sai da gaskiya ta zo masa alhali shi yana cikin kogon Hira, sai Mala'ika ya zo masa sai ya ce: Ka yi karatu, ya ce: «‌Ni ba mai karatu ba ne» ya ce: «‌Sai ya kamani sai ya rufeni har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ni ba mai karatu ba ne, sai ya kamani sai ya rufeni karo na biyu har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta Ya halicci mutum daga gudan jini ka yi karatu alhali Ubangijinka shi ne mafi girma}», [al-Alaƙ: 1-3]. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo da su (ayoyin) zuciyarsa tana karkarwa, sai ya shiga wurin Nana Khadija 'yar Kuwailid - Allah Ya yarda da ita -, sai ya ce: «‌Ki lulluɓeni, ki lulluɓeni» sai suka lulluɓe shi, har sai da razani ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari: «‌Haƙiƙa na ji tsoron kaina» sai Nana Khadija ta ce: A'a wallahi, Allah ba zai kunyataka ba har abada, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar ɗawainiya kana bawa wanda ba shi da komai, kana tarbar baƙo, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya, sai Nana Kahadija ta tafi da shi har ta zo da shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, ɗan kawun Nana Khadija. Ya kasance wani mutum ne da ya zama kirista a zamanin jahiliyya, kuma ya kasance yana rubuta harshen Ibraniyanci, yana rubuta Linjila da harshen Ibraniyanci abinda Allah Ya so ya rubuta, kuma ya kasance dattijo ne makaho, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawuna na ! Ka ji magana daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana me ka gani? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta masa labarin da ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Namus ne (Mala'ika) wanda Allah Ya saukarwa (Annabi) Musa shi, kaicona inama dai a ce ni matashi ne a cikin kwanukan da za'a aikoka, inama dai a ce ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin yanzu su zasu koreni?», ya ce: Eh, babu wani mutumin da zai zo da irin abinda ka zo da shi sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah kuma bai jima zuwa wani lokaci ba ya rasu, kuma wahayi ya yanke.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3]

Bayani

Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa farkon abinda aka farawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne mafarki na gaskiya a cikin bacci, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya hakan ya zo a bayyane mai kama da hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaitaka, ya kasance yana kaɗaitaka a kogon Hira sai ya yi bauta a cikin wasu 'yan darare ƙididdigaggu kafin ya koma ga iyalinsa, kuma ya tafi da guzuri saboda hakan, sannan ya dawo gurin Uwar muminai Nana Khadija - Allah Ya yarda da ita - sai ya yi guziri ga kwatankwacin adadin dararen, har sai da umarni na gaskiya ya zo masa alhali shi yana kogon Hira. Sai Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo masa sai ya ce masa: Ka yi karatu, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ban iya karatu ba, ya ce: Sai ya kamani ya damƙeni ya matseni har sai da yakaini ƙololuwa a wahala sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, nace: Ban iya karatu ba, sai ya kamani ya damƙeni karo na biyu har sai da yakai ƙololuwa a wahalar da ni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ban iya karatu ba, sai ya kamani a karo na uku sai ya damƙeni karo na uku sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne Mafi gima}. [al-Alaƙ: 1-3]. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya dawo da ayoyin zuciyarsa tana karkarwa dan jin tsoron mutuwa, sai ya shiga wurin matarsa Uwar muminai Nana Khadija 'yar Khuwailid - Allah ya yarda da ita -, sai ya ce: ki lulluɓeni da tufafi, sai suka lulluɓe shi da tufafi har sai da tsoron ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari, kuma ya ce: Haƙiƙa na ji wa kaina tsoron mutuwa, sai Nana Khadija ta ce: A'a, wallahi har abada Allah ba zai kunyataka ba, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar nauyin mai rauni wanda ba zai iya tsayuwa da kansa ba, kana bawa talaka wanda ba shi da komai; inda kake baiwa mutane abinda ba za su same shi ba a wurin waninka ba, kuma kana tarbar baƙi, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya. Sai Nana Khadija ta tafi da shi har kai shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, shi ɗan kawunta ne, kuma ya kasance mutum ne da ya bar jahiliyya ya kasance kirista, ya kasance yana rubuta abinda Allah Ya so ya rubuta na Injila da harshen Ibraniyanci, kuma ya kasance dattijo ne mai yawan shekaru, ba ya gani, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawu, ka ji daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana, me kake gani? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ba shi labarin abinda ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Jibril ne wanda Allah Ya saukar da shi ga AnnabinSa Musa - aminci ya tabbata agare shi -, kaicona a ce ni matashi ne ƙaƙƙarfa a cikinsu (kwanukan da za'a aikoka), inama dai a ce zan zama ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai (Manzo) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Shin su zasu koreni?! Ya ce: Eh, babu wani mutum da ya zo da abinda ka zo da shi ba sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah bai rayu tsawon lokaci ba sai ya rasu, kuma wahayi ya yi jinkiri tsawon lokaci.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin farkon wahayi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Mafarkin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana daga jumlar rabe-raben wahayi.
  3. Halaccin yin guzuri, kuma shi baya kore dogaro ga Allah, haƙiƙa shugaban masu dogaro ga Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙi guzuri.
  4. Cikar karamcinSa - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - cewa Shi Ya sanar da bayinSa abinda basu sani ba, kuma Ya cire su daga duhun jahilci zuwa hasken ilimi.
  5. Falalar sanin rubutu; saboda abinda ke cikinsa na abubuwan amfani masu girma waɗanda ba zasu ƙirgu ba; dan da su ne aka rubuta ilimummuka, kuma aka taskance hikimomi, aka kiyaye labarun mutanen farko, aka kiyaye Litattafan Allah saukakku, kuma al'amuran Addini da duniya suka tabbata.
  6. Farkon abinda ya sauka na Alƙur'ani {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta} [al-Alaƙ: 1].
  7. Kyawawan ɗabi'u, da ɗabi'un alheri sababi ne na aminci daga mummuan hatsari, da nau'ikan abubuwan ƙi, wanda alherinsa ya yi yawa to ƙarshensa zai yi kyau, kuma an yi masa fatan kuɓutar Addini da duniya.
  8. Halaccin yabon mutum a gabansa dan maslaha.
  9. Yana kamata kwantar da hankalin wanda tsoro ya same shi da kuma yi masa bushara, da ambata masa sabubban kuɓuta.
  10. Mafi girman dalili kuma mafi isuwar hujja akan cikar Nana Khadija - Allah Ya yarda da ita -, da girman hangen nesanta, da ƙarfin ranta, da girman fahimtarta, haƙiƙa a siffantawarta ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta tattara dukkan nau’ukan tushen manyan ɗabi'u, kuma iyayen (ɗabi'u), domin kyautatawa kodai zuwa ga makusanta, ko zuwa ga na nesa, ko da jiki, ko da dukiya, kuma ko dai ga wanda yake ya tsayu da kansa, ko ga waninsa, kuma ta yalwata magana a matsayin da ya dace dan yawaitawa.
  11. Wanda wani al'amari ya fada masa to an so ya faɗawa wanda ya aminta da nasiharsa da kuma ingancin tunaninsa.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin