+ -

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ: مَرَرْنَا مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى الْحِجْرِ، فَقَالَ لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَدْخُلُوا مَسَاكِنَ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ، إِلَّا أَنْ تَكُونُوا بَاكِينَ؛ حَذَرًا أَنْ يُصِيبَكُمْ مِثْلُ مَا أَصَابَهُمْ» ثُمَّ زَجَرَ فَأَسْرَعَ حَتَّى خَلَّفَهَا.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2980]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun wuce tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan Hijr (gidajen Samudawa), sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana:
"Kada ku shiga mazaunan waɗanda suka zalinci kawunansu, sai dai idan kun kasance kuna masu kuka; dan kiyayewa kada abinda ya samesu ya sameku". Sannan ya tsawatar sai ya yi gaggawa har ya wuce wurin ya tura shi baya.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2980]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - lokacin da ya wuce gidajen Samudawa ya yi hani akan shiga gidajen waɗanda ake yi wa azaba waɗanda suka zalinci kawunansu ko zowa gidajen, saidai idan mai shiga ɗin ya zama yana mai kuka yana mai izina da su; dan jin tsoron abinda ya samesu na azaba ya same shi, sannan ya zaburi dabbarsa sai ya gaggauta har saida ya ƙetare su.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tinani a kan halayen waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya halakar da su, da kaucewa akan abinda suka afka cikinsa; da kiyayewa daga rafkana daga jujjuya ma'anonin ayoyi.
  2. Gidajen Samudawa waɗanda ake yi wa azaba ba'a zama a wurin bayan su Samudawan, kuma ba'a riƙunsu a matsayin ƙasar zama; domin wanda ke zaune a cikinsu ba zai yi wu koda yaushe a ce kuka yake yi ba, alhali an yi hani daga shiga sai da wannan siffar.
  3. Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan kula a yayin wucewa ta gidajen azzalumai, da wuraren azaba, misalinsa yin gaggawa a Wadi Muhassir; domin ma'abota giwa sun halaka a wannan wurin, to ya kamata ga mai tafiya a irin waɗannan wuraren ya kula ya ji tsoro da kuka, da yin izina da su da kuma halakarsu, kuma ya nemi tsarin Allah daga hakan.
  4. Hanin da kuma gargaɗarwar ya ƙunshi mazaunan Samudawa da wasunsu daga waɗanda ke cikin ma'anarsu na ragowar al'ummu waɗanda azaba ta saukar musu.
  5. Hani daga riƙon waɗannan wurare dan yawon shaƙatawa da makamancin hakan.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin