عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: يُؤْذِينِي ابْنُ آدَمَ يَسُبُّ الدَّهْرَ وَأَنَا الدَّهْرُ، بِيَدِي الأَمْرُ أُقَلِّبُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4826]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: Ɗan Adam ya cutar da Ni yana zagin zamani alhali Nine zamani, al'amari yana hannunNa iNa jujjuya dare da rana».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4826]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi: Mutumin da yake zagin zamani a lokacin saukar masifu da abubuwan ƙi yana cuta ta kuma yana tauyeNi; domin cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne Mai jujjuya al'amura Shi kaɗai, kuma Mai sarrafa abinda yake faruwa; to aibata zamani aibata Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, zamani kuwa kawai shi halitta ne abin horewa, abubuwa suna gudana ne a cikinsa da umarnin Allah - Maɗaukakin sarki -.