عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ:
«لَا يَمْنَعَنَّ رَجُلًا مِنْكُمْ مَخَافَةُ النَّاسِ أَنْ يَتَكَلَّمَ بِالْحَقِّ إِذَا رَآهُ أَوْ عَلِمَهُ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [مسند أحمد: 11403]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai kada tsoron mutane ya hana ɗayanku faɗin gaskiya idan ya ganta ko ya santa».
[Ingantacce ne] - - [مسند أحمد - 11403]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa sahabbansa huɗuba, daga cikin abinda ya yi musu wasicci da shi cewa kada tsoro da kwarjinin mutane da kuma ƙarfinsu ya hana musulmi faɗin gaskiya ko umarni da ita idan ya ganta ko ya santa.