عن أبي بكر الصديق رضي الله عنه قال: يا أيُّها النَّاس، إِنَّكُم لَتَقرَؤُون هذه الآية: (يَا أَيُّها الَّذِين آمَنُوا عَلَيكُم أَنفسَكُم لاَ يَضُرُّكُم مَنْ ضَلَّ إِذَا اهْتَدَيتُم) [المائدة: 105]، وَإِنِّي سمِعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ النَّاس إِذا رَأَوُا الظَّالِمَ فَلَم يَأْخُذُوا عَلَى يَدَيه أَوشَكَ أَنْ يَعُمَّهُمُ اللهُ بِعِقَابٍ مِنْهُ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه وأحمد]
المزيــد ...
Daga (Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: yaku mutane, lallai ku kuna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lazimci kawunanku wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya}, lallai ni na ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi".
[Ingantacce ne] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2168]
(Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari: Cewa mutane suna karanta wannan ayar:
{Yaku waɗanda suka yi imani ku lizimci kawunanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya} [al-Ma'ida: 105].
Suna fahimta daga ayar cewa ya wajaba ga mutum ya yi ƙoƙari ya gyara kansa kawai, kuma ɓatan wanda ya ɓata ba zai cutar da shi ba bayan hakan, kuma su ba’a nema daga gare su su yi umarni da kyakkyawa kuma su hana mummuna ba.
Sai ya sanar da su cewa ita ayar ba haka take ba, cewa shi ya ji annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai mutane idan suka ga azzalimi ba su hana shi zalincin ba, kuma suna da iko akan hana shin, ya kusa Allah Ya game su baki ɗaya da uƙuba daga gareShi, mai aikata abin ƙin, da mai yin shiru bai hana ba.