عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«قَارِبُوا وَسَدِّدُوا، وَاعْلَمُوا أَنَّهُ لَنْ يَنْجُوَ أَحَدٌ مِنْكُمْ بِعَمَلِهِ» قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ وَلَا أَنْتَ؟ قَالَ: «وَلَا أَنَا، إِلَّا أَنْ يَتَغَمَّدَنِيَ اللهُ بِرَحْمَةٍ مِنْهُ وَفَضْلٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2816]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2816]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da sahabbai akan su yi aiki, kuma su ji tsoron Allah gwargwadan ikonsu, ba tare da zurfafawa ko Gazawa ba, kuma su nufi daidai da aikinsu ta hanyar ikhlasi ga Allah da bin sunna dan a karɓi aikinsu sai su zama sababi ga saukar rahama garesu.
Sannan ya ba su labarin cewa wani mutum aikinsa kawai ba zai tseratar da shi ba; kai babu makawa daga rahamar Allah.
Suka ce: Har kai Ya Manzon Allah aikinka ba zai tseratar da kai ba tare da girman darajarsa?
Sai ya ce: Har ni, sai dai in Allah Ya suturtani da falalar rahamarSa.