Gida
kashe kashe
Dangane da Wannan katafaren Aiki
Android App
iOS App
kirayemu
Yare
Karkasawa:
Gida
kashe kashe
Sirah da Tarihi
Tarihin Annabi
kase kashen kana nan rassa
lis din Hadisai
Farkon abinda aka fara wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da shi na wahayi shi ne kyakkyawan mafarki a cikin barci*, ya kasance ba ya ganin mafarki sai ya zo masa kwatankwacin hasken Asuba, sannan aka sa masa son kaɗaici, ya kasance yana kaɗaita a kogon Hira, sai ya yi ibada a cikinsa - shi ne ibada - a wasu ƙididdigaggun darare kafin ya koma gurin iyalansa, kuma yana yin guziri saboda hakan, sannan ya koma ga Nana Khadija, sai ya yi guzuri na kwatankwacinsu (kwanukan), har sai da gaskiya ta zo masa alhali shi yana cikin kogon Hira, sai Mala'ika ya zo masa sai ya ce: Ka yi karatu, ya ce: «Ni ba mai karatu ba ne» ya ce: «Sai ya kamani sai ya rufeni har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: Ka yi karatu, sai na ce: Ni ba mai karatu ba ne, sai ya kamani sai ya rufeni karo na biyu har sai da ya kai ƙololuwar wahala gareni sannan ya sakeni, sai ya ce: {Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta* Ya halicci mutum daga gudan jini* ka yi karatu alhali Ubangijinka shi ne mafi girma}», [al-Alaƙ: 1-3]. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya dawo da su (ayoyin) zuciyarsa tana karkarwa, sai ya shiga wurin Nana Khadija 'yar Kuwailid - Allah Ya yarda da ita -, sai ya ce: «Ki lulluɓeni, ki lulluɓeni» sai suka lulluɓe shi, har sai da razani ya tafi daga gare shi, sai ya faɗawa Nana Khadija kuma ya bata labari: «Haƙiƙa na ji tsoron kaina» sai Nana Khadija ta ce: A'a wallahi, Allah ba zai kunyataka ba har abada, lallai kai kana sadar da zumunci, kana ɗaukar ɗawainiya kana bawa wanda ba shi da komai, kana tarbar baƙo, kuma kana taimako akan masifu na gaskiya, sai Nana Kahadija ta tafi da shi har ta zo da shi wurin Waraƙah ɗan Naufal ɗan Asad ɗan Abdul'uzza, ɗan kawun Nana Khadija. Ya kasance wani mutum ne da ya zama kirista a zamanin jahiliyya, kuma ya kasance yana rubuta harshen Ibraniyanci, yana rubuta Linjila da harshen Ibraniyanci abinda Allah Ya so ya rubuta, kuma ya kasance dattijo ne makaho, sai Nana Khadija ta ce da shi: Ya kai ɗan kawuna na ! Ka ji magana daga ɗan ɗan'uwanka, sai Waraƙah ya ce masa: Yakai ɗan ɗan'uwana me ka gani? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta masa labarin da ya gani, sai Waraƙah ya ce masa: Wannan Namus ne (Mala'ika) wanda Allah Ya saukarwa (Annabi) Musa shi, kaicona inama dai a ce ni matashi ne a cikin kwanukan da za'a aikoka, inama dai a ce ina raye lokacin da mutanenka zasu koreka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Shin yanzu su zasu koreni?», ya ce: Eh, babu wani mutumin da zai zo da irin abinda ka zo da shi sai an cutar da shi, idan lokacinka ya riskeni zan taimakeka taimako mai ƙarfi. Sannan Waraƙah kuma bai jima zuwa wani lokaci ba ya rasu, kuma wahayi ya yanke.
عربي
Turanci
Indonisiyanci
...
Sinhalese
Vietnam
Hausa
Portuguese
Swahili
Yaran Tailand
Asami
الهولندية
الغوجاراتية
الرومانية
المجرية
الجورجية
×
kirayemu
Suna *
E- mail *
Wasika *
Aika
E- mail
()
*
Yin rijisa
×
Yare:
العربية
English
اردو
Español
Bahasa Indonesia
ئۇيغۇرچە
বাংলা
Français
Türkçe
Русский
Bosanski
සිංහල
हिन्दी
中文
فارسی
Tiếng Việt
Tagalog
Kurdî
Hausa
Português
മലയാളം
తెలుగు
Kiswahili
தமிழ்
မြန်မာ
ไทย
Deutsch
日本語
پښتو
অসমীয়া
Shqip
Svenska
አማርኛ
Nederlands
ગુજરાતી
Кыргызча
नेपाली
Yorùbá
Lietuvių
دری
Српски
Soomaali
тоҷикӣ
Kinyarwanda
Română
Magyar
Čeština
Moore
Malagasy
Fulfulde
Italiano
Oromoo
ಕನ್ನಡ
Wolof
Български
Azərbaycan
Ελληνικά
Akan
O‘zbek
Українська
ქართული
Lingala
Македонски
ភាសាខ្មែរ
×
Bincike a cikin:
العربية
English
اردو
Español
Bahasa Indonesia
ئۇيغۇرچە
বাংলা
Français
Türkçe
Русский
Bosanski
සිංහල
हिन्दी
中文
فارسی
Tiếng Việt
Tagalog
Kurdî
Hausa
Português
മലയാളം
తెలుగు
Kiswahili
தமிழ்
မြန်မာ
ไทย
Deutsch
日本語
پښتو
অসমীয়া
Shqip
Svenska
አማርኛ
Nederlands
ગુજરાતી
Кыргызча
नेपाली
Yorùbá
Lietuvių
دری
Српски
Soomaali
тоҷикӣ
Kinyarwanda
Română
Magyar
Čeština
Moore
Malagasy
Fulfulde
Italiano
Oromoo
ಕನ್ನಡ
Wolof
Български
Azərbaycan
Ελληνικά
Akan
O‘zbek
Українська
ქართული
Lingala
Македонски
ភាសាខ្មែរ
Bincike
×
Sakamakon Bincike: