عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«كُلُّ سُلَامَى مِنَ النَّاسِ عَلَيْهِ صَدَقَةٌ، كُلَّ يَوْمٍ تَطْلُعُ فِيهِ الشَّمْسُ تَعْدِلُ بَيْنَ الِاثْنَيْنِ صَدَقَةٌ، وَتُعِينُ الرَّجُلَ فِي دَابَّتِهِ فَتَحْمِلُهُ عَلَيْهَا أَوْ تَرْفَعُ لَهُ عَلَيْهَا مَتَاعَهُ صَدَقَةٌ، وَالكَلِمَةُ الطَّيِّبَةُ صَدَقَةٌ، وَكُلُّ خُطْوَةٍ تَمْشِيهَا إِلَى الصَّلَاةِ صَدَقَةٌ، وَتُمِيطُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ صَدَقَةٌ».
[صحيح] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية: 26]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Dukkanin gaɓa ta mutane sadaka ce gare shi, kowanne yinin da rana ta hudu a cikinsa ka daidaita tsakanin mutum biyu sadaka ne, ka taimaki mutum a dabbarsa ka ɗora shi a kanta ko ka sauke masa kayansa daga kanta to sadaka ne, kalma mai daɗi sadaka ce, dukkanin takun da ka yi zuwa masallaci sadaka ne, ka kauda ƙazanta akan hanya sadaka ne».
[Ingantacce ne] - [رواه البخاري ومسلم] - [الأربعون النووية - 26]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa akwai sadaka ta ɗawwu'i saboda Allah - Maɗaukakin sarki - akan kowanne musulmi mukallafi a kowacce rana a kan kowacce gaba daga cikin gabban jikinsa, sadaka ta Nafila ga Allah madaukakin sarki akan tafarkin godiya gare Shi akan lafiya, kuma sanya ƙasusuwansa gaɓɓai zai samu dama da suna damƙa da shinfiɗawa. kuma cewa wannan sadakar tana kaiwa ga ayyukan alheri gabaɗayanta bata tsayuwa akan bada wata dukiya, Daga ciki: Daidaitawarka da yin sulhunka tsakanin masu husuma sadaka ne. A taimakonka ga wani gajiyayye a dabbarsa (abin hawa) sai ka ɗora shi akanta, ko ka ɗauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai daɗi ta zikiri ce da addu'a da sallama da wasunsu sadaka ce. Kowanne takin da ka yi tafiya da shi zuwa sallah sadaka ne, kawar da abinda ake cutuwa da shi a hanya sadaka ne.