عن أنس بن مالك رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ أَحَبَّ أَنْ يُبْسَطَ لَهُ فِي رِزْقِهِ، وَيُنْسَأَ لَهُ فِي أَثَرِهِ، فَلْيَصِلْ رَحِمَهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5986]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda yake so a yalwata masa a arzikinsa, kuma a jinkirta masa a rayuwarsa, to, ya sadar da zumuncinsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5986]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana kwaɗaitarwa a kan sa da zumuncin 'yan uwa ta hanyar ziyara da girmamawar jiki da dukiya da makamancin hakan, kuma cewa su sababi ne a yalwatar arziki da tsawon rai.