+ -

عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا شَيْءٌ أَثْقَلُ فِي مِيزَانِ الْمُؤْمِنِ يَوْمَ القِيَامَةِ مِنْ خُلُقٍ حَسَنٍ، وَإِنَّ اللَّهَ لَيُبْغِضُ الفَاحِشَ البَذِيءَ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي] - [سنن الترمذي: 2002]
المزيــد ...

Daga Abu Darda - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu wani abu mafi nauyi a ma'aunin mumini a ranar Alkiyama daga kyawawan dabi'u, lallai Allah Yana kin mai alfasha mai mummunar magana".

Ingantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi nauyin abinda ke ma'aunin mumini ranar Alkiyama na ayyuka da maganganu shi ne kyawawan dabi'u, hakan ta hanyar sakin fuska, da barin cutarwa, da yin alheri. Allah - Madaukakin sarki - Yana kin mai munanawa a aikinsa da maganarsa, mai munanawa a abinda harshensa yake furtawa da shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية القيرقيزية النيبالية اليوروبا الدرية الصومالية المالاجاشية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar kyawawan dabi'u; domin cewa shi yana gadar da soyayyar Allah ga mai shi, da kuma soyayyar bayin Allah, shi ne mafi girman abinda ake aunawa a ranar Alkiyama.