عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لاَ يَنْظُرُ اللَّهُ إِلَى مَنْ جَرَّ ثَوْبَهُ خُيَلاَءَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5783]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5783]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga sakin tufafi ko gwabso ƙasan idan sawu dan jiji da kai da kuma girman kai, kuma cewa wanda ya aikata hakan ya kasance ya cancanci narko mai tsanani cewa Allah ba Zai yi duba zuwa gareshi ba duba na rahama a ranar alƙiyama.