+ -

عَنْ يحيى بنِ عُمَارةَ المَازِنِيِّ قَالَ:
شَهِدْتُ عَمْرَو بْنَ أَبِي حَسَنٍ سَأَلَ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ زَيْدٍ، عَنْ وُضُوءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَدَعَا بِتَوْرٍ مِنْ مَاءٍ، فَتَوَضَّأَ لَهُمْ وُضُوءَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَكْفَأَ عَلَى يَدِهِ مِنَ التَّوْرِ، فَغَسَلَ يَدَيْهِ ثَلاَثًا، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فِي التَّوْرِ، فَمَضْمَضَ وَاسْتَنْشَقَ وَاسْتَنْثَرَ، ثَلاَثَ غَرَفَاتٍ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَغَسَلَ وَجْهَهُ ثَلاَثًا، ثُمَّ غَسَلَ يَدَيْهِ مَرَّتَيْنِ إِلَى المِرْفَقَيْنِ، ثُمَّ أَدْخَلَ يَدَهُ فَمَسَحَ رَأْسَهُ، فَأَقْبَلَ بِهِمَا وَأَدْبَرَ مَرَّةً وَاحِدَةً، ثُمَّ غَسَلَ رِجْلَيْهِ إِلَى الكَعْبَيْنِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 186]
المزيــد ...

Daga Yahaya dan Umara AlMazinu ya ce:
Na halarci Amr dan Abu Hassan ya tambayi Abdullahi dan Zaid game da alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce a kawo masa kwarya ta ruwa, sai ya yi musu alwala irin alwalar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya sanya hannunsa akwaryar, sai ya wanke hannayensa sau uku, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar, sai ya kuskure baki ya shaka ruwa ya face, kanfata uku, sannan ya shigar da hannunsa sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya wanke hannayensa sau biyu zuwa gwiwar hannu, sannan ya shigar da hannunsa sai ya shafi kansa, sai ya yi gaba da su ya yi baya sau daya, sannan ya wanke kafafuwansa zuwa idan sawu.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 186]

Bayani

Abdullahi Dan Zaid - Allah Ya yarda da shi - yana bayyana siffar alwalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi a aikace, sai ya nemi karamar kwarya (buta) ta ruwa, a farko sai ya fara da wanke tafukansa, sannan ya karkatar da kwaryar ya zuba ruwa sai ya wankesu sau uku a wajen kwaryar, sannan ya shigar da hannunsa a cikin kwaryar ya kanfato daga gareta kanfata uku yana kuskurar baki a kowacce kanfata yana shaka ruwa yana facewa, sannan ya kanfato daga kwaryar (butar) sai ya wanke fuskarsa sau uku, sannan ya kanfato daga gareta sai ya wanke hannayensa zuwa gwiwoyin hannaye sau biyu-biyu, sannan ya shigar da hannayensa cikin kwaryar, ya shafi kansa da hannayensa ya fara da magabacin kansa har ya kai zuwa keyarsa saman wuya, sannan ya dawo da su har ya kai gurin da ya fara daga gare shi, sannan ya wanke kafafuwansa tare da idan sawu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. yanayin malami shi ne mafi kusancin hanyoyi zuwa fahimta da tabbatar da ilimi, daga hakan koyarwa a aikace.
  2. halaccin maimaitawa sau uku a wasu daga gabobin alwala da yi sau biyu a sashinsu, wajibi (shi ne) sau daya.
  3. Wajabcin jerantawa tsakanin gabban alwala kamar yadda ya zo a cikin hadisin.
  4. Iyakar fuska daga matsirar gashin kai na al'ada zuwa abinda ya sauka daga gemu da haba a tsawo, daga kunne zuwa kunne a fadi.