+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا اسْتَيْقَظَ أَحَدُكُمْ مِنْ مَنَامِهِ فَلْيَسْتَنْثِرْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، فَإِنَّ الشَّيْطَانَ يَبِيتُ عَلَى خَيَاشِيمِهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 238]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 238]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya farka daga baccinsa cewa ya face hancinsa sau uku; facewa ita ce fitar da ruwa daga hanci bayan shigar da shi, hakan domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hanci - shi ne hancin gaba ɗayansa -.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An shar'antawa dukkan wanda ya farka daga bacci ya face hanci dan gusar da gurbin Shaiɗan daga hancinsa, idan ya kasance zai yi alwala, to umarnin ya fi ƙarfafuwa a lokacin.
  2. Face hanci yana daga cikar fa'idar shaƙa ruwa; domin shaƙa ruwa tsarkake cikin hanci ne, facewa kuma hakan yana fitar da datti tare da ruwan.
  3. Ƙayyade shi da baccin dare, dan yin riƙo daga lafazin "yana kwana"; domin kwana ba ya kasancewa sai daga baccin dare, kuma cewa shi ne lokacin zatan tsawaitawa da zirfafawa.
  4. A cikin hadisin akwai dalili akan cakuɗuwar Shaiɗan ga mutum alhali shi ba ya jin hakan.