عَنْ لَقِيطِ بْنِ صَبِرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كُنْتُ وَافِدَ بَنِي الْمُنْتَفِقِ -أَوْ فِي وَفْدِ بَنِي الْمُنْتَفِقِ- إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: فَلَمَّا قَدِمْنَا عَلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمْ نُصَادِفْهُ فِي مَنْزِلِهِ، وَصَادَفْنَا عَائِشَةَ أُمَّ الْمُؤْمِنِينَ، قَالَ: فَأَمَرَتْ لَنَا بِخَزِيرَةٍ، فَصُنِعَتْ لَنَا، قَالَ: وَأُتِينَا بِقِنَاعٍ -وَالْقِنَاعُ: الطَّبَقُ فِيهِ تَمْرٌ- ثُمَّ جَاءَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «هَلْ أَصَبْتُمْ شَيْئًا؟ أَوْ أُمِرَ لَكُمْ بِشَيْءٍ؟» قَالَ: قُلْنَا: نَعَمْ، يَا رَسُولَ اللَّهِ، قَالَ: فَبَيْنَا نَحْنُ مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ جُلُوسٌ، إِذْ دَفَعَ الرَّاعِي غَنَمَهُ إِلَى الْمُرَاحِ، وَمَعَهُ سَخْلَةٌ تَيْعَرُ، فَقَالَ: «مَا وَلَّدْتَ يَا فُلَانُ؟»، قَالَ: بَهْمَةً، قَالَ: «فَاذْبَحْ لَنَا مَكَانَهَا شَاةً»، ثُمَّ قَالَ: «لَا تَحْسِبَنَّ» وَلَمْ يَقُلْ: لَا تَحْسَبَنَّ «أَنَّا مِنْ أَجْلِكَ ذَبَحْنَاهَا، لَنَا غَنَمٌ مِائَةٌ لَا نُرِيدُ أَنْ تَزِيدَ، فَإِذَا وَلَّدَ الرَّاعِي بَهْمَةً، ذَبَحْنَا مَكَانَهَا شَاةً» قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ لِي امْرَأَةً وَإِنَّ فِي لِسَانِهَا شَيْئًا -يَعْنِي الْبَذَاءَ- قَالَ: «فَطَلِّقْهَا إِذن»، قَالَ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّ لَهَا صُحْبَةً، وَلِي مِنْهَا وَلَدٌ، قَالَ: «فَمُرْهَا» يَقُولُ: عِظْهَا، «فَإِنْ يَكُ فِيهَا خَيْرٌ فَسَتَفْعَلْ، وَلَا تَضْرِبْ ظَعِينَتَكَ كَضَرْبِكَ أُمَيَّتَكَ» فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَخْبِرْنِي عَنِ الْوُضُوءِ، قَالَ: «أَسْبِغِ الْوُضُوءَ، وَخَلِّلْ بَيْنَ الْأَصَابِعِ، وَبَالِغْ فِي الِاسْتِنْشَاقِ إِلَّا أَنْ تَكُونَ صَائِمًا».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي وابن ماجه] - [سنن أبي داود: 142]
المزيــد ...
Daga Laƙiɗ Bin Sabirah -Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance ɗan aiken Banul Muntafiƙi - ko a cikin jama'ar Bunul Muntafiƙi - zuwa wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Lokacin da muka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bamu same shi agidansa ba, sai muka samu Nana A'isha uwar muminai, ya ce:
Sai ta yi umarni a bamu farfesu, sai aka dafa mana, ya ce: Kuma aka zo mana da ƙina' - ƙina: Shi ne farantin da a cikinsa akwai dabino - sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «Shin kun samu wani abu ne? ko shin an yi umarni akawo muku wani abu ne?» ya ce: Mukace: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da mai kiwo ya kora tumakansa zuwa garke, atare da shi akwai wani 'yar akuya tana kuka, sai ya ce: «Kai wane me aka haifa maka?», ya ce: 'Yar akuya, ya ce: «To ka yanka mana babbar akuya a madadinta», Sannan ya ce: «Kada ka zaci» bai ce: kada ka zaci «Mu saboda kaine muka yankata ba, muna da tumakai ɗari, bama so su ƙaru, idan aka haifawa makiyayin 'yar akuya, sai mu yanka babbar akuya a madadinta» Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai ni ina da wata mata, akwai wani abu a harshenta - yana nufin bata iya magana ba - ya ce: «To ka saketa», ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai sahabiya ce, kuma ina da ɗa tare da ita, ya ce: «To ka umarceta» Yana cewa ka yi mata wa'azi, «Idan akwai alheri a tare da ita zata aikata, kada ka daki matarka kamar yadda kake dukan baiwarka», sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labari game da alwala, ya ce: «Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne».
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 142]
Laƙiɗ Ibnu Sabira - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tare da waninsa daga mutanensa Banul Muntafiƙ, ya ce: Bamu same shi a gidansa ba, sai muka samu Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sai ta yi umarni a yi mana farfesu na gari da romo, kuma aka kawo mana farantin da a cikinsa akwai dabino. Sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: Shin an kawo muku wani abu ne na abinci? Muka ce: Eh, Laƙiɗ ya ce: Muna zaune tare da shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga mai kiwon tumakan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana korosu zuwa gurin kwanciyarsu, kuma yana ɗauke da jaririn ɗan bunsuru yana kuka, sai ya ce: Me aka haifa maka? Ya ce: Mace. Ya ce: To ka yanka mana wata akuyar babba a madadinta, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Kada ka yi zatan cewa mu saboda ku ne muka ɗorawa kanmu muka yanka muku ba, kawai mu muna da wasu tumakai ne guda ɗari, bama son adadin ya ƙaru akan wannan adadin, idan aka haifi sabon jinjiri sai mu yanka wani a madadinsa, Laƙiɗ ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai cewa matata mai dogon harshe ce kuma mai alfasha ce, ya zan yi da ita? Ya ce: To ka saketa kawai. Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah lallai tana tare da ni tuntuni, kuma akwai zuriya a tsakakninmu. Ya ce: To ka yi mata wa'azi, idan akwai alheri a tare da ita to zata ji wa'azinka, idan bata ji wa’azinba to ka daketa dukan da bazai sa rauni ba, kada ka daketa kamar yadda kake dukan bayinka. Sannan Laƙiɗ ya ce: Ya Manzon Allah, ka bani labari game da alwala. Ya ce: Ka isar da ruwa bigirensa a lokacin alwala, kuma ka cikawa kowace gaɓa haƙƙinta, kada ka bar wani abu daga cikin farillan alwala da sunnoninta, ka rarraba yatsun hannayenka da ƙafafuwanka a lokacin wanketa, kuma ka kai matuƙa a shaka ruwa a cikin hancinka a lokacin alwala da kuma fitar da shi saidai idan ka kasance ka ƙulla alwala dan kada ruwa ya shiga cikinka.