عَنْ جَابِرٍ رضي الله عنه قال: أَخْبَرَنِي عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ:
أَنَّ رَجُلًا تَوَضَّأَ فَتَرَكَ مَوْضِعَ ظُفُرٍ عَلَى قَدَمِهِ فَأَبْصَرَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «ارْجِعْ فَأَحْسِنْ وُضُوءَكَ» فَرَجَعَ، ثُمَّ صَلَّى.
[صحيح بشواهده] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 243]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Umar Dan Alkhaddab ya bani labari:
Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah.
[Ingantacce ne a baki dayan Riwayoyin sa] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 243]
Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya gama alwalarsa, sai ya bar gwargwadan farce a ƙafarsa (Lam’a) ruwa bai same shi ba, sai ya ce masa yana mai nuni zuwa gurin da bai sami ruwa ba: Ka koma ka kyautata alwalarka ka cikata ka ba wa kowacce gaba haƙƙinta na ruwa. Sai mutumin ya koma ya cika alwalarsa, sannan ya yi sallah.