عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَغْسِلُ، أَوْ كَانَ يَغْتَسِلُ، بِالصَّاعِ إِلَى خَمْسَةِ أَمْدَادٍ، وَيَتَوَضَّأُ بِالْمُدِّ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 201]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 201]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wankan janaba da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu. Sa'i: Mudu haɗu, mudu kuma: Gwargwadan cikin tafuka biyu na mutum madaidaicin halitta.