عَنْ عُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ رضي الله عنه قَالَ: كَانَتْ عَلَيْنَا رِعَايَةُ الْإِبِلِ فَجَاءَتْ نَوْبَتِي فَرَوَّحْتُهَا بِعَشِيٍّ فَأَدْرَكْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَائِمًا يُحَدِّثُ النَّاسَ فَأَدْرَكْتُ مِنْ قَوْلِهِ:
«مَا مِنْ مُسْلِمٍ يَتَوَضَّأُ فَيُحْسِنُ وُضُوءَهُ، ثُمَّ يَقُومُ فَيُصَلِّي رَكْعَتَيْنِ، مُقْبِلٌ عَلَيْهِمَا بِقَلْبِهِ وَوَجْهِهِ، إِلَّا وَجَبَتْ لَهُ الْجَنَّةُ» قَالَ فَقُلْتُ: مَا أَجْوَدَ هَذِهِ، فَإِذَا قَائِلٌ بَيْنَ يَدَيَّ يَقُولُ: الَّتِي قَبْلَهَا أَجْوَدُ، فَنَظَرْتُ فَإِذَا عُمَرُ قَالَ: إِنِّي قَدْ رَأَيْتُكَ جِئْتَ آنِفًا، قَالَ: «مَا مِنْكُمْ مِنْ أَحَدٍ يَتَوَضَّأُ فَيُبْلِغُ - أَوْ فَيُسْبِغُ - الْوَضُوءَ ثُمَّ يَقُولُ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ إِلَّا فُتِحَتْ لَهُ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ الثَّمَانِيَةُ يَدْخُلُ مِنْ أَيِّهَا شَاءَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 234]
المزيــد ...
Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna kiwon raƙuma sai zagayena ya zo sai na korosu garke da daddare sai na riski Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye yana karantar da mutane sai na riska faɗinsa:
"Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi" Ya ce: Sai na ce: Ya mamakin kyan wannan, sai ga wani mai magana a gabana yana cewa: Wacce ke gabanta ta fi kyau, sai na duba sai ga Umar ya ce: Lallai ni na ganka ka zo ɗazu, ya ce: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sai ya kai matuƙa - ko sai ya cika - alwalar sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne sai an buɗe masa kofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 234]
Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya yi bayani alhali shi yana zantar da mutane falala biyu masu girma:
Na farko: Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar ya cikata ta fuskar da aka sunnanta, kuma ya ba kowace gaɓa haƙƙinta na ruwa, sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne; sai an buɗe masa ƙofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so.
Na biyu: Wanda ya yi wannan alwalar cikakkiya, sannan ya tashi bayan alwalar ya yi sallah raka'a biyu; yana mai fuskantosu da zuciyarsa da ikhlasi da ƙanƙar da kai, ya ƙanƙar dakai da fuskarsa da dukkan gaɓɓan jikinsa saboda Allah, sai aljanna ta wajaba gare shi.