عَنْ مَعْدَانَ بْنِ أَبِي طَلْحَةَ الْيَعْمَرِيُّ قَالَ:
لَقِيتُ ثَوْبَانَ مَوْلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: أَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ أَعْمَلُهُ يُدْخِلُنِي اللهُ بِهِ الْجَنَّةَ؟ أَوْ قَالَ قُلْتُ: بِأَحَبِّ الْأَعْمَالِ إِلَى اللهِ، فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ فَسَكَتَ. ثُمَّ سَأَلْتُهُ الثَّالِثَةَ فَقَالَ: سَأَلْتُ عَنْ ذَلِكَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «عَلَيْكَ بِكَثْرَةِ السُّجُودِ لِلَّهِ، فَإِنَّكَ لَا تَسْجُدُ لِلَّهِ سَجْدَةً، إِلَّا رَفَعَكَ اللهُ بِهَا دَرَجَةً، وَحَطَّ عَنْكَ بِهَا خَطِيئَةً» قَالَ مَعْدَانُ: ثُمَّ لَقِيتُ أَبَا الدَّرْدَاءِ فَسَأَلْتُهُ فَقَالَ لِي: مِثْلَ مَا قَالَ لِي: ثَوْبَانُ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 488]
المزيــد ...
Daga Ma’adan ɗan Abu Dalha Al-Ya'amury ya ce:
Na gamu da Sauban 'yantaccen bawan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na ce: Ka ba ni labari da wani aikin da zan aikata shi Allah Ya shigar da ni Aljanna da shi? ko ya ce, na ce: Da mafi son ayyuka zuwa ga Allah, sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi, sai ya yi shiru, sannan na tambaye shi a karo na uku sai ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan, sai ya ce: "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita" Ma'adan ya ce: Sannan na gamu da Abu al-Darda'i sai na tambaye shi sai ya fada min abinda Sauban ya faɗa mini.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 488]
An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin da zai zama sababin shiga aljanna, ko game da mafi soyuwar ayyuka a wurin Allah?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce wa mai tambayar: Ka lazimci yawan sujjada a cikin sallah, domin kai ba za ka yi wa Allah sujjada ba sai Ya ɗaga darajarka da ita, kuma Ya kankare kurakuranka da ita.