عن ابن عباس رضي الله عنهما مرفوعاً: «عَيْنَانِ لاَ تَمسُّهُمَا النَّار: عَيْنٌ بَكَتْ من خَشْيَة الله، وعَيْنٌ بَاتَت تَحْرُسُ في سَبِيل الله».
[صحيح] - [رواه الترمذي]
المزيــد ...
A kan Ibn Abbas - Allah ya yarda da shi - tare da dagawa: "Idanun da wuta ba za ta iya taba su ba: ido mai kuka saboda tsoron Allah, da kuma ido mai kiyaye hanyar Allah."
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]
Ma'anar hadisin: Wuta ba ta taba ido mai kuka saboda tsoron Allah Madaukaki, yayin da mutum ya tuna girman Allah da ikonsa na bautar da bayinsa da tuna halin da yake ciki da kuma gazawarsa cikin gaskiyar Allah Madaukaki. Yana kuka da begen rahamar sa da kuma tsoron azabarsa da fushin sa, saboda wannan anyi alkawarin samun kubuta daga wuta. Da kuma wani ido wanda wuta bata taba shi ba, wanda shine: Duk wanda ya kiyaye saboda Allah Madaukakin Sarki a bude da wuraren fada domin kiyaye rayukan musulmai. Da kuma fadinsa: "Wuta ba ta taba su ba." Wannan daga furucin sashi ne da nufin duka, kuma abin da ake nufi shi ne cewa duk wanda ya yi kuka saboda tsoron Allah Madaukaki da wanda ya kiyaye a tafarkin Allah, Allah Madaukaki ya hana jikinsu zuwa wuta.