عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«مَنْ قَالَ: لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ المُلْكُ وَلَهُ الحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ، كَانَتْ لَهُ عَدْلَ عَشْرِ رِقَابٍ، وَكُتِبَتْ لَهُ مِائَةُ حَسَنَةٍ، وَمُحِيَتْ عَنْهُ مِائَةُ سَيِّئَةٍ، وَكَانَتْ لَهُ حِرْزًا مِنَ الشَّيْطَانِ يَوْمَهُ ذَلِكَ حَتَّى يُمْسِيَ، وَلَمْ يَأْتِ أَحَدٌ بِأَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ بِهِ إِلَّا أَحَدٌ عَمِلَ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3293]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini, yana da abinda ya yi daidai da wuyaye goma, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari, kuma za'a shafe masa mummuna ɗari, kuma za ta kasance tsari daga Shaiɗan a wannan yinin nasa, har sai ya kai maraice, kuma ba wanda zai zo da abin da ya fi wanda ya zo da shi, saidai wanda ya aikata sama da hakan».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3293]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya) babu wani abin bauta da cancanta (sai Allah, Shi kaɗai Yake) a cikin UluhiyyarSa da RububiyyarSa da sunayenSa da kuma siffofinSa, (mulki naSa ne) da tasarrufi da kuma jujjuya al'amura gaba ɗayansa, (godiya taSa ce) akan dukkan abinda Ya halicce shi kuma Ya ƙaddara shi, (Shi Mai iko ne akan dukkan komai) ba tare da wani mai hanawa ko mai karewa ba, abinda bai so ba zai kasance ba. Wanda ya faɗi wannan zikirin sau ɗari a yini kuma ya maimaita shi, za'a rubuta masa lada a wurin Allah kamar ya 'yanta wuyaye goma ne, kuma za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari da daraja ɗari a cikin aljanna, kuma za'a shafe masa za'a sarayar masa da mummuna ɗari, kuma zasu zame masa tsari da kiyayewa da katanga da hani daga Shaiɗan da halakarwarsa da kuma rinjayensa a wannan yinin nasa har sai ya shiga yammaci ta hanyar faɗauwar rana, kuma wani ba zai zo da mafificin abinda ya zo dashi ba sai dai wanda ya aikata hakan kuma ya ƙari a kansa.