+ -

عَن أَبي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ قَالَ: رَضِيتُ بِاللَّهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا، وَجَبَتْ لَهُ الْجَنَّةُ».

[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 1529]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayinAddini, kuma da Muhammad a matsayin Manzo, Aljanna ta wajaba a gare shi».

[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 1529]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Na yarda da Allah a matsayin Ubangiji) kuma abin bautawa da gaskiya mai reno kuma mamallaki shugaba kuma mai gyarawa. (Da Musulunci) da dukkanin hukunce-hukuncensa na umarni da hani (Addini) kuma tafarki da shari'a da miƙa wuya. (Da Annabi Muhammad a matsayin manzo) da Annabi; da dukkanin abinda aka aiko shi da shi kuma ya isar da shi garemu, sai aljanna ta wajaba gare shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa a kan faɗar wannan addu'ar, da bayanin ladan da ya jerantu a kanta.
  2. Yarda da Allah a matsayin Ubangiji ta ƙunshi kada mutum ya bautawa waninSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
  3. Yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Annabi da Manzo ya ƙunshi yi masa biyayya - aminci ya tabbata agare shi - da jawuwa ga sunnarsa.
  4. Yarda da Musulunci a matsayin Addini shi ne yarda da abinda Allah Ya zaɓe shi ga bayinSa.
  5. An so faɗin wannan addu'ar a yayin shahada biyu daga jin kiran sallah kamar yanda yake a cikin wasu riwayoyin daban.
  6. Kuma ya zo a cikin wani hadisin daban cewa an so wannan addu'ar a safiya da maraice.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Rashanci Sinhalese Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية الرومانية المجرية الموري Malagasy الولوف الأوكرانية الجورجية المقدونية الخميرية الماراثية
Manufofin Fassarorin