عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ أَحَبَّ أَسْمَائِكُمْ إِلَى اللهِ عَبْدُ اللهِ وَعَبْدُ الرَّحْمَنِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2132]
المزيــد ...
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai ne mafi soyuwar sunayenku a wurin Allah (su ne) Abdullahi da Abdurrahman".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2132]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar sunaye a wurin Allah su ne a ambaci namiji da: Abdullahi, ko: Abdurrahman.