عَنْ جَابِرٍ رَضيَ اللهُ عنهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ، غُرِسَتْ لَهُ نَخْلَةٌ فِي الجَنَّةِ».
[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3464]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Tsarki ya tabbata ga Allah da yabonSa, za a dasa masa bishiyar dabino a cikin aljanna».
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3464]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah) Ya tsarkakeShi (Mai girma) da zatinSa da siffofinSa da kuma ayyukanSa (da yabonSa) abin haɗawa da raɓa siffofin cika gareShi - tsarki ya tabbatar maSa -; za'a kafa kuma za'a dasa masa wani dabino a cikin ƙasar aljanna a duk lokacin da ya faɗeta.