عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَقُولُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَنَا عِنْدَ ظَنِّ عَبْدِي، وَأَنَا مَعَهُ حِينَ يَذْكُرُنِي، فَإِنْ ذَكَرَنِي فِي نَفْسِهِ ذَكَرْتُهُ فِي نَفْسِي، وَإِنْ ذَكَرَنِي فِي مَلَإٍ ذَكَرْتُهُ فِي مَلَإٍ خَيْرٍ مِنْهُ، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ شِبْرًا، تَقَرَّبْتُ إِلَيْهِ ذِرَاعًا، وَإِنِ اقْتَرَبَ إِلَيَّ ذِرَاعًا، اقْتَرَبْتُ إِلَيْهِ بَاعًا، وَإِنْ أَتَانِي يَمْشِي أَتَيْتُهُ هَرْوَلَةً».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2675]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2675]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana cewa:
Ni ina inda zatan bawaNa gareNi yake, zan yi mu'amala da bawaNa gwargwadan zatansa da Ni, hakan dan ƙauna da burin rangwami, kuma Ina yi masa abinda yake tinanin afkuwarsa daga gareNi na alheri ne ko wanin hakan; kuma Ni ina tare da shi da rahama da dacewa da shiriya da kiyayewa da ƙarfafawa idan ya anbaceNi.
Idan ya anbaceNi a cikin ransa shi kaɗai a kaɗaice da tasbihi da hailala ko waninsu; zan anbace shi a cikin raiNa.
Idan ya anbaceNi a cikin jama'a; zan ambace shi a cikin jama'ar da tafisu yawa kuma ta fisu tsarki.
Wanda ya nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadan taki Allah Zai yi masa ƙari sai Ya kusanto zuwa gare shi da zira'i.
Idan ya nemi kusanci zuwa gare shi gwargwadan zira'i zai kusanto zuwa gare shi gwargwadan awon faɗin hannaye.
Idan ya zo zuwa ga Allah yana tafiya to Allah zai zo masa Yana sassarfa.
Bawa idan ya nemi kusanci zuwa ga Ubangijinsa da biyayya gareShi da fuskantowa gareShi, to lallai Ubangiji - Maɗaukakin sarki - Zai ƙara kusanci zuwa gareshi dan sakamako daga jinsin aikinsa.
A duk lokacin da bautar mumini ta cika ga Ubangijinsa to Allah Maɗaukakin sarki zai kusanto zuwa gare shi, kyautar Allah da sakamakonSa (ita ce ) mafi yawa daga aikin bawa da kuma wahalarsa, a taƙaice cewa sakamakon Allah mai rinjaya ne akan aiki ta hanyar kaifiyya da kuma kimmiya.
Mumini yana kyautata zato, kuma yana aiki, yana gaggawa yana ƙarawa har ya gamu da Allah.