عَنْ سَعْدِ بنِ أبي وَقَّاصٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَيَعْجِزُ أَحَدُكُمْ أَنْ يَكْسِبَ، كُلَّ يَوْمٍ أَلْفَ حَسَنَةٍ؟» فَسَأَلَهُ سَائِلٌ مِنْ جُلَسَائِهِ: كَيْفَ يَكْسِبُ أَحَدُنَا أَلْفَ حَسَنَةٍ؟ قَالَ: «يُسَبِّحُ مِائَةَ تَسْبِيحَةٍ، فَيُكْتَبُ لَهُ أَلْفُ حَسَنَةٍ، أَوْ يُحَطُّ عَنْهُ أَلْفُ خَطِيئَةٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2698]
المزيــد ...
Daga Sa'ad ɗan Abu Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya ce
Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: «Shin ɗayanku zai gaza wajen samun kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?» Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: «Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2698]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin ɗayanku zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana? Sai ɗaya daga cikin mazauna a gurinsa ya ce: Ta yaya mutum zai iya samun kyakkyawan lada dubu a kowace rana cikin sauƙi? Ya ce: To ya ce: "Subhanal Lahi". sau ɗari; sai a rubuta masa kaykkyawa dubu; domin cewa kyakkyawa ɗaya da kwatankwacinsa goma ne, ko kuma a kankare masa mummuna dubu daga cikin munanan ayyukansa.