+ -

عَنْ أَبِي مُوسَى رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَثَلُ الَّذِي يَذْكُرُ رَبَّهُ وَالَّذِي لاَ يَذْكُرُ رَبَّهُ، مَثَلُ الحَيِّ وَالمَيِّتِ»، ولفظ مسلم: «مَثَلُ الْبَيْتِ الَّذِي يُذْكَرُ اللهُ فِيهِ، وَالْبَيْتِ الَّذِي لَا يُذْكَرُ اللهُ فِيهِ، مَثَلُ الْحَيِّ وَالْمَيِّتِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6407]
المزيــد ...

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce", lafazin Muslim kuma: "Misalin gidan da ake ambatan Allah a cikinsa, da gidan da ba'a ambatan Allah a cikinsa, kamar rayayye ne da matacce".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6407]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana banbanci tsakanin wanda yake ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - da wanda ba ya ambatanSa, kuma misalin banbanci ne tsakanin rayayye da matacce a anfaninsa da kyakkyawan zahirinsa, misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa misalin rayayye ne wanda a zahirinsa mai adone da hasken rayuwa, kuma baɗininsa da hasken ma'arifa, kuma a cikinsa akwai anfani, kuma misalin wanda ba ya ambatan Allah kwatankwacin mamaci ne wanda zahirinsa ba ya anfani, kuma baɗininsa ɓataccene, babu wani anfani acikinsa.
Haka nan gidan da ake siffanta shi da rayayye idan mazaunansa sun kasance suna ambatan Allah, inba haka ba to shi mataccen gida ne, saboda barin mazaunansa daga ambatan Allah; idan an wawaita mamaci da matacce a cikin siffanta gida kawai ana nufi da shi mazaunin gidan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan ambatan Allah da gargaɗarwa daga rafkana daga gare shi.
  2. Zikiri shi ne rayuwar rai, kamar yadda rai rayuwar jiki ne.
  3. Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.
  4. Al-Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin gida, kuma cewa kada a wofantar da shi daga zikiri.
  5. Al-Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa tsawon rayuwa a cikin ɗa'a falala ce koda mamacin yana cirata zuwa alheri; domin rayayye zai risku da shi kuma zai ƙaru a kansa da abinda ya aikata shi na ayyukan ɗa'a.