عَنْ أَبِي مُسْلِمٍ الْخَوْلَانِيِّ، قَالَ: حَدَّثَنِي الْحَبِيبُ الْأَمِينُ، أَمَّا هُوَ فَحَبِيبٌ إِلَيَّ، وَأَمَّا هُوَ عِنْدِي فَأَمِينٌ، عَوْفُ بْنُ مَالِكٍ الْأَشْجَعِيُّ رضي الله عنه قَالَ:
كُنَّا عِنْدَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، تِسْعَةً أَوْ ثَمَانِيَةً أَوْ سَبْعَةً، فَقَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» وَكُنَّا حَدِيثَ عَهْدٍ بِبَيْعَةٍ، فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» فَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: «أَلَا تُبَايِعُونَ رَسُولَ اللهِ؟» قَالَ: فَبَسَطْنَا أَيْدِيَنَا وَقُلْنَا: قَدْ بَايَعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللهِ، فَعَلَامَ نُبَايِعُكَ؟ قَالَ: «عَلَى أَنْ تَعْبُدُوا اللهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَالصَّلَوَاتِ الْخَمْسِ، وَتُطِيعُوا -وَأَسَرَّ كَلِمَةً خَفِيَّةً- وَلَا تَسْأَلُوا النَّاسَ شَيْئًا» فَلَقَدْ رَأَيْتُ بَعْضَ أُولَئِكَ النَّفَرِ يَسْقُطُ سَوْطُ أَحَدِهِمْ، فَمَا يَسْأَلُ أَحَدًا يُنَاوِلُهُ إِيَّاهُ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1043]
المزيــد ...
Daga Abu Muslim Al-Khaulani ya ce: Masoyi amintacce ya zantar dani, amma shi to masoyi ne gareni, amma shi a wajena to amintaccene, Awf Dan Malik Al-Ashja'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (Mu) tara ko takwas ko bakwai, sai ya ce: "Shin ba kwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" mun kasance farkon yin caffa (mubaya’a) sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan ya ce: "Shin bakwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan Ya ce: "Shin bakwa wa Manzon Allah caffa ba?" Ya ce: Sai muka shimfida hannayenmu muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai" Hakika na ga sashin wadancan mutanan bulalar dayansu tana faduwa, amma ba ya tambayar wani ya miko masa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1043]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wani adadi na sahabbai sai ya nemi su yi masa caffa su yi masa alkawari akan lazimtar wasu al'amura har sau uku:
Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi.
Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare.
Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai.
Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su.
Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.