عَنْ أُمِّ قَيْسٍ بِنْتِ مِحْصَنٍ رَضيَ اللهُ عنها:
أَنَّهَا أَتَتْ بِابْنٍ لَهَا صَغِيرٍ لَمْ يَأْكُلِ الطَّعَامَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَجْلَسَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي حَجْرِهِ، فَبَالَ عَلَى ثَوْبِهِ، فَدَعَا بِمَاءٍ، فَنَضَحَهُ وَلَمْ يَغْسِلْهُ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 223]
المزيــد ...
Daga Ummu Kais Bint Mihsan -Allah Ya yarda da ita -:
Cewa ita ta zo da wani ɗanta ƙarami bai fara cin abinci ba zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai ya yi fitsari akan tufafinsa, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan bai wanke shi ba.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 223]
Ummu Kais bintu Mihsan - Allah Ya yarda da shi - ta zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani ɗanta wanda bai fara cin abinci ba saboda ƙanƙantar shekarunsa, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya zaunar da shi a ƙirjinsa, sai yaron ya yi fitsari akan tufafinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya sa a kawo masa ruwa, sai ya yayyafa ruwan akan tufafinsa bai wanke tufafin ba.