عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَشَدَّ حَيَاءً مِنَ العَذْرَاءِ فِي خِدْرِهَا، فَإِذَا رَأَى شَيْئًا يَكْرَهُهُ عَرَفْنَاهُ فِي وَجْهِهِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6102]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6102]
Abu Sa'idul Khudr - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga yarinya budurwa wacce bata yi aure ba, ba ta yi mu'amala da maza ba wacce ke suturce a cikin gidanta, yana daga tsananin kunyarsa cewa shi idan ya ki wani abu fuskarsa tana canjawa kuma ba ya magana, kai sahabbansa suna fahimtar kinsa ga hakan a fuskarsa.