عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِي مَا حَدَّثَتْ بِهِ أَنْفُسَهَا، مَا لَمْ تَعْمَلْ أَوْ تَتَكَلَّمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5269]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5269]
Annabi - tsira da amincin Allah su abbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi ba'a kama shi da zancen zuci na sharri kafin ya aikata shi ko ya fade shi, yayin da Allah Ya ɗauke ƙunci kuma Ya yi afuwa, bai riƙi al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da abinda aka samu a cikin tinani da kaikawo a cikin zuciya ba, tare da ya nutsu gare shi kuma ya tabbata a wurinsa ba; idan ya tabbata a cikin zuciyarsa kamar girman kai ko taƙama ko munafunci ko ya yi aiki da gaɓɓansa ko ya faɗa da harshensa to cewa shi za'a kamashi da hakan.