+ -

عن تميم الداري رضي الله عنه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«الدِّينُ النَّصِيحَةُ» قُلْنَا: لِمَنْ؟ قَالَ: «لِلهِ وَلِكِتَابِهِ وَلِرَسُولِهِ وَلِأَئِمَّةِ الْمُسْلِمِينَ وَعَامَّتِهِمْ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 55]
المزيــد ...

Daga Tamim al-Dari - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Addini nasiha ne" Muka ce; ga wa? Ya ce; "Ga Allah da littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmai da dukkaninsu".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 55]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa addini a tsaye yake a kan ikhlasi da gaskiya, har a yi kamar yadda Allah Ya wajabta, cikakke ba tare da tawaya ko algus ba.
Sai aka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ga wa nasihar za ta kasance? sai ya ce:
Na farko: Nasiha ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya daukaka -: ta hanyar tsarkake aiki gareshi, da rashin haɗa wani da Shi, kuma mu yi imani da Rububiyyarsa da Uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa, da girmama al'amarinsa, da kira zuwa imani da Shi.
Na biyu: Nasiha ga littafinsa shi ne Al-ƙur'ani mai girma: Shi ne cewa mu ƙudirce cewa shi zancensa ne, kuma ƙarshen littattafansa, kuma cewa shi mai shafewa ne ga dukkanin shari'o'i kafinsa, mu girmamashi, mu karantashi haƙiƙanin karantashi, mu yi aiki da muhkam ɗinsa, mu miƙa wuya ga abubuwa masu kamanceceniya a cikinsa, kuma mu kore tawilin masu karkacewa gareshi, mu wa'azantu da wa'azozinsa, da yaɗa ilimummukansa, da kira zuwa gareshi.
Na uku: Nasiha ga manzonsa (Annabi) muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Shi ne mu kudire cewa shi ne karshen manzanni, mu gasgatashi a cikin abin da ya zo da shi, mu kamanta umarninsa, mu nisanci haninsa, kuma kada mu bautawa Allah da komai sai abin da ya zo da shi, mu girmama haƙƙinsa, mu girmamashi, mu yaɗa da'awarsa, mu yaɗa shari'arsa, kuma mu kore tuhuma daga gareshi.
Na hudu: Nasiha ga shugabannin musulmai: Ta hanyar taimakonsu a kan gaskiya, da rashin jayayya da su a al'amari, da ji da biyayya garesu a cikin biyayya ga Allah.
Na biyar: Nasiha ga musulami: Ta hanyar kyautatawa zuwa garesu da kiransu, da kame cuta daga garesu, da son alheri garesu, da taimakekeniya tare da su a kan biyayya da tsoron Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Umarni da nasiha ga kowa da kowa.
  2. Girman matsayin nasiha a addini.
  3. Addini ya ƙunshi ƙudirce-ƙudirce da maganganu da ayyuka.
  4. Yana daga cikin nasiha tsarkake zuciya daga algus ga wanda aka yi wa nasihar da kuma nufin alheri gareshi.
  5. Kyakkyawan koyarwar Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da yake ambaton abu a dunkule sannan ya yi shi dalla-dalla.
  6. Farawa da mafi muhimmanci sannan mai bi masa, yayin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara da nasiha ga Allah, sannan littafinsa, sannan manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ga shugabannin musulmai, sannan kowa da kowansu.