عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الرَّضَاعَةُ تُحَرِّمُ مَا تُحَرِّمُ الوِلَادَةُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [الأربعون النووية: 44]
المزيــد ...
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce:
«Shayarwa tana haramta dukkan abin da haihuwa take haramtawa».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [الأربعون النووية - 44]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abin da haihuwa da nasaba suke haramtawa na yakumbo (Inna) ce ko baffa ko ɗan uwa...to shayarwa tana haramta shi, kuma shayarwa tana halatta abin da haihuwa take halattawa na hukunce-hukunce.