عَنِ النَّوَّاسِ بْنِ سِمْعَانَ الْأَنْصَارِيِّ رضي الله عنه قَالَ:
سَأَلْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الْبِرِّ وَالْإِثْمِ، فَقَالَ: «الْبِرُّ حُسْنُ الْخُلُقِ، وَالْإِثْمُ مَا حَاكَ فِي صَدْرِكَ، وَكَرِهْتَ أَنْ يَطَّلِعَ عَلَيْهِ النَّاسُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2553]
المزيــد ...
Daga Nawwas ɗan Sam'an alAnsari - Allah Ya yarda da shi ya ce:
Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga aikin alheri da kuma zunubi, sai ya ce: "Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2553]
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin alheri da zunubi, sai ya ce:
Mafi girman ɗabi'un aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a tare da Allah da tsoron Allah, da kuma halitta, tare da halitta da jure wa cuta, da ƙarancin fushi, da shinfiɗa fuska, da daddaɗan zance, da sadarwa da ɗa'a da tausayi da kuɓutarwa da kyakkyawar mu'amala da abokantaka.
Amma zunubi abinda ya motsu a cikin rai daga abubuwa masu rikitarwa kuma ya yi kai kawo ba tare da ƙirji ya buɗe gare shi ba, kuma kokwanto ya faru daga gare shi, da tsoron kasancewarsa zunubi, baka so ka bayyanar da shi ba, dan kasancewarsa mummuna ga idanuwa da mutanen kirki da cikakkunsu, hakan domin cewa rai da ɗabi'arta ƙarƙashin tsinkayen mutane akan alherinta, idan ka ƙi tsinkaye akan sashin ayyukanta to shi zunubi ne babu alheri a cikinsa.