عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا مِنْ مُسْلِمٍ يَدْعُو بِدَعْوَةٍ لَيْسَ فِيهَا إِثْمٌ، وَلَا قَطِيعَةُ رَحِمٍ، إِلَّا أَعْطَاهُ اللهُ بِهَا إِحْدَى ثَلَاثٍ: إِمَّا أَنْ تُعَجَّلَ لَهُ دَعْوَتُهُ، وَإِمَّا أَنْ يَدَّخِرَهَا لَهُ فِي الْآخِرَةِ، وَإِمَّا أَنْ يَصْرِفَ عَنْهُ مِنَ السُّوءِ مِثْلَهَا» قَالُوا: إِذنْ نُكْثِرُ، قَالَ: «اللهُ أَكْثَرُ».
[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 11133]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa".
[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 11133]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa; Musulmi idan ya roƙi Allah ya roke shi wata bukata wacce ba zunubi ba ce kamar ya roƙeShi da sawwaƙa saɓo da zalinci, kuma bai yi addu'a da yanke zumunci ba; kamar ya yi mummunar addu'a akan 'ya'yansa da 'yan uwansa, sai Allah Ya ba shi ɗayan al'amura uku da addu'arsa: Kodai Ya gaggauto masa da addu'arsa Ya ba shi abinda ya roƙa. Ko kuma Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya jinkirtar masa da ita dan lada gare shi a ranar alƙiyama da ɗaukaka daraoji, ko rahama ko gafarta munanan ayyuka. Ko kuma Ya kawar masa a duniyarsa da mummuna kwatankwacinta da gwargwadan addu'ar. Sai sahabban suka cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ai sai mu yawaita addu'a; dan mu samu waɗannan falalolin? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai abinda ke gurin Allah shi ya fi yawa kuma ya fi girma daga abinda kuke tambaya, kyautarSa bata ƙarewa, kuma bata tiƙewa.