عَنِ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها زَوْجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
أَنَّ الْحَوْلَاءَ بِنْتَ تُوَيْتِ بْنِ حَبِيبِ بْنِ أَسَدِ بْنِ عَبْدِ الْعُزَّى مَرَّتْ بِهَا وَعِنْدَهَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقُلْتُ: هَذِهِ الْحَوْلَاءُ بِنْتُ تُوَيْتٍ، وَزَعَمُوا أَنَّهَا لَا تَنَامُ اللَّيْلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تَنَامُ اللَّيْلَ! خُذُوا مِنَ الْعَمَلِ مَا تُطِيقُونَ، فَوَاللهِ لَا يَسْأَمُ اللهُ حَتَّى تَسْأَمُوا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 785]
المزيــد ...
Daga Nana A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:
Lallai cewa Haula'a Bint Tuwait Ibnu Habib Ibnu Asad Ibnu Abdul'uzza ta wuceta alhali Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana wurinta, sai na ce:
Wannan Haula'u ce Bnit Tuwait, kuma sun yi da'awar cewa bata baccin dare, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Bata baccin dare! Ku dinga aikata aikin da zaku iya, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa har sai kun ƙosa».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 785]
Haula'u Bnt Tuwait - Allah Ya yarda da ita - ta kasance a wurin uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo gurinta (Nana A'isha), sai (Haula'u) ta fita ta barta Sai Nana A'isha ta ce masa: Wannan matar bata baccin dare, kai tana raya shi da sallah. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce yana mai tsananin yi mata inkari: Bata baccin dare! ku shagalta da aiki na gari wanda zaku iya dawwama a kansa, na rantse da Allah, Allah ba Ya ƙosawa akan baiwa bayinSa salihai masu biyayya lada da sakamako akan biyayyarsu da kuma kyawawan ayyukansu da kuma ayyukansu na gari har sai sun ƙosa sun bar aikin.