عن أبي هريرة رضي الله عنه: أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«يَنْزِلُ رَبُّنَا تَبَارَكَ وَتَعَالَى كُلَّ لَيْلَةٍ إِلَى السَّمَاءِ الدُّنْيَا حِينَ يَبْقَى ثُلُثُ اللَّيْلِ الْآخِرُ، يَقُولُ: «مَنْ يَدْعُونِي فَأَسْتَجِيبَ لَهُ؟ مَنْ يَسْأَلُنِي فَأُعْطِيَهُ؟ مَنْ يَسْتَغْفِرُنِي فَأَغْفِرَ لَهُ؟».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1145]
المزيــد ...
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1145]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayanin Allah maɗaukaki Yana sakkowa a kowanne dare zuwa sama makusanciya lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura, yana kwaɗaitar da bayinSa a kan su roƙe shi, shi kuma zai amsawa wanda ya roƙe Shi, yana zaburar da su a kan su tambaye Shi abin da suke so, Shi kuma zai ba wanda ya tambaye Shi, yana kiransu da su roƙi gafararSa daga zunubansu Shi kuma yana gafartawa bayinSa muminai.