عَنْ أُبَيِّ بْنِ كَعْبٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كَانَ رَجُلٌ لَا أَعْلَمُ رَجُلًا أَبْعَدَ مِنَ الْمَسْجِدِ مِنْهُ، وَكَانَ لَا تُخْطِئُهُ صَلَاةٌ، قَالَ: فَقِيلَ لَهُ: أَوْ قُلْتُ لَهُ: لَوْ اشْتَرَيْتَ حِمَارًا تَرْكَبُهُ فِي الظَّلْمَاءِ، وَفِي الرَّمْضَاءِ، قَالَ: مَا يَسُرُّنِي أَنَّ مَنْزِلِي إِلَى جَنْبِ الْمَسْجِدِ، إِنِّي أُرِيدُ أَنْ يُكْتَبَ لِي مَمْشَايَ إِلَى الْمَسْجِدِ، وَرُجُوعِي إِذَا رَجَعْتُ إِلَى أَهْلِي، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «قَدْ جَمَعَ اللهُ لَكَ ذَلِكَ كُلَّهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 663]
المزيــد ...
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take wuce shi, ya ce: Sai aka ce masa: Ko nace masa: Ai da za ka sayi jakin da zaka dinga hawan shi cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son gidana ya kasance a gefen masallaci, lallai ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wadannan gaba ɗayan su».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 663]
Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa wani mutum daga cikin mutanen Madina yana daga cikin mafi nisan gida daga masallacin Annabi, kuma ya kasance sallah bata wuce shi; kai yana halattar kowace sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai aka ce masa: Inama dai a ce zaka sayi jakin da zaka dinga hawansa a cikin duhun dare da kuma cikin zafin ƙasa a cikin rana, ya ce: Bana son a ce gidana yana gefen masallaci, lallai ni ina son Allah Ya rubuta mini tafiyata zuwa masallaci, da kuma dawowata idan na dawo zuwa ga iyalaina, sai maganarsa ta kai wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: «Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka hakan baki ɗayansu».