عَن قُطْبَةَ بنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ مُنْكَرَاتِ الأَخْلاَقِ وَالأَعْمَالِ وَالأَهْوَاءِ».
[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3591]
المزيــد ...
Daga Ƙuɗbah ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa:
«Ya Allah lallai ni ina neman tsarinKa, daga munanan ɗabi'u da ayyuka da soye-soyen rayuka».
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 3591]
Ya kasance daga cikin addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Ya Allah lallai ni ina neman tsari) ina fakewa (da Kai) banda waninKa, (daga munanan) abubuwan da Allah da ManzonSa suka hana su, (ɗabi'u) kamar ƙullata da hassada da girman kai, (da kuma) munanan (ayyuka) kamar zagi, (da) dukkanin (soye-soyen zuciya), waɗanda zuciya take son su alhali sun saɓawa shari'a.