عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ، حُطَّتْ خَطَايَاهُ وَإِنْ كَانَتْ مِثْلَ زَبَدِ الْبَحْرِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6405]
المزيــد ...
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6405]
Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da gode masa. an share kurakuransa an kuma gafarta su, ko da suna da yawa misalin farar kunfar nan ce da take saman teku lokacin kaɗawar igiya da ambaliya.