عن أبي أيوب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ قَالَ: لَا إلَهَ إلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ عَشْرَ مَرَّاتٍ كَانَ كَمَنْ أَعْتَقَ أَرْبَعَةَ أَنْفُسٍ مِنْ وَلَدِ إسْمَاعِيلَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
An rawaito daga Abu Ayyub -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Duk wanda ya ce Babu wani Ubangiji Sai Allah shi kadai wanda bashi da abokin tarayya, Mulki nasa ne, kuma godima tasa ce, kuma shi mai iko ne akan komai zai kasance Kamar wanda ya 'yanta Rayuka Hudu daga cikin 'ya'yan Annabi Isma'il
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Hadisin Dalili ne kan falalar wannan zikiri saboda abunda yake cikinsa na kadaita Alla, kuma lallai cewa duk wanda ya fade shi sau goma yana Masani mai aiki da abinda ya kunsa yana da lada kwatankwacin wanda ya Yanta Bayi Hudu na Zuriyar Annabi Isma'il Dan Sayyidina Ibrahim -Amincin Allah a gare su.