+ -

عن معاوية رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول:
«مَنْ يُرِدِ اللهُ بِهِ خَيْرًا يُفَقِّهْهُ فِي الدِّينِ، وَإِنَّمَا أَنَا قَاسِمٌ، وَاللهُ يُعْطِي، وَلَنْ تَزَالَ هَذِهِ الْأُمَّةُ قَائِمَةً عَلَى أَمْرِ اللهِ، لَا يَضُرُّهُمْ مَنْ خَالَفَهُمْ، حَتَّى يَأْتِيَ أَمْرُ اللهِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 71]
المزيــد ...

Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa;
Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 71]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ba da labarin cewa wanda Allah Ya nufe shi da alheri, to, sai ya azurta shi da fahimta a addininSa tsarki ya tabbata a gare shi. Kuma shi [Annabi] tsira da aminci su tabbata a agare shi Mai rabawa ne, yana raba abin da Allah Ya ba shi na arziki da ilimi da wanin haka, Kuma hakikanin wanda yake bayarwar shi ne Allah, amma duk wanda ba shi ba, to, su sabubba ne, ba sa anfanarwa sai da izinin Allah, Kuma lalle wannan al’ummar ba za ta gushe a kan al’amarin Allah ba, wanda ya saɓa musu ba zai taba cutar da su ba , har ƙiyama ta tashi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girma da falalar ilimin addini, da koyon shi da kuma kwaɗaitarwa a kansa.
  2. Tsayuwa a kan gaskiya tabbace yake a cikin wannan al’ummar, idan wata jama'a ta kauce sai wata ta ɗauka.
  3. Fahimtar addini yana daga cikin nufatar Allah maɗaukaki na alheri ga bawansa.
  4. Annabi tsara da amincin Allah su tabbata a gare shi kawai yana bayarwa ne da umarnin Allah da ganin damarSa, shi ba ya mallakar komai.