عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ اللهَ طَيِّبٌ لَا يَقْبَلُ إِلَّا طَيِّبًا، وَإِنَّ اللهَ أَمَرَ الْمُؤْمِنِينَ بِمَا أَمَرَ بِهِ الْمُرْسَلِينَ، فَقَالَ: {يَا أَيُّهَا الرُّسُلُ كُلُوا مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَاعْمَلُوا صَالِحًا، إِنِّي بِمَا تَعْمَلُونَ عَلِيمٌ} [المؤمنون: 51] وَقَالَ: {يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُلُوا مِنْ طَيِّبَاتِ مَا رَزَقْنَاكُمْ} [البقرة: 172] ثُمَّ ذَكَرَ الرَّجُلَ يُطِيلُ السَّفَرَ أَشْعَثَ أَغْبَرَ، يَمُدُّ يَدَيْهِ إِلَى السَّمَاءِ: يَا رَبِّ، يَا رَبِّ، وَمَطْعَمُهُ حَرَامٌ، وَمَشْرَبُهُ حَرَامٌ، وَمَلْبَسُهُ حَرَامٌ، وَغُذِيَ بِالْحَرَامِ، فَأَنَّى يُسْتَجَابُ لِذَلِكَ؟».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1015]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Yaku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce: {Yaku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
[al-Mu'uminun: 51] .
Kuma Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku} [al:Baƙara: 172] sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1015]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah tsarkakakke ne, tsarkakakke abin tsarkakewa daga nakasa kowacce iri da aibuka, kuma Mai siffantuwa ne da cika, ba Ya karɓar ayyuka da maganganu da ƙudirce-ƙudirce sai abinda ya kasance mai tsarki, shi ne tsantsa saboda Allah, wanda ya dace da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, baya kamata a nemi kusanci zuwa ga Allah sai da hakan, daga mafi girman abinda tsarkin ayyuka yake faruwa ga mumini tsarkin abin cinsa, kuma ya zama na halal ne, da hakan ne aikinsa zai tsarkaka, saboda haka ne Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci manzanni da shi, na cin halal da aiki na gari, sai Ya ce: {Yaku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa} kuma Ya ce: {Yaku wadanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirtaku}.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu:
Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan.
Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne.
Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a.
Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji!
A tare da waɗannan sabubban na amsa addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!