عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يَبْسُطُ يَدَهُ بِاللَّيْلِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ النَّهَارِ، وَيَبْسُطُ يَدَهُ بِالنَّهَارِ لِيَتُوبَ مُسِيءُ اللَّيْلِ، حَتَّى تَطْلُعَ الشَّمْسُ مِنْ مَغْرِبِهَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2759]
المزيــد ...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2759]
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuba daga bayinSa. Idan bawa ya yi laifi da rana kuma ya tuba da daddare Allah Zai karbi tubansa, idan ya yi laifi da daddare ya kuma tuba da rana Allah Zai karɓi tubansa. Kuma tsarki ya tabbatar maSa Yana shinfiɗa hannunSa dan tuba dan farin ciki da tuban, da kuma karɓar tuban, ƙofar tuba tana nan a bude har sai rana ta ɓullo daga yammacinta dan alamtar wa da ƙarewar duniya, idan ta ɓullo to za'a kulle ƙofar tuba.