عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِلْأَشَجِّ أَشَجِّ عَبْدِ الْقَيْسِ: «إِنَّ فِيكَ خَصْلَتَيْنِ يُحِبُّهُمَا اللهُ: الْحِلْمُ، وَالْأَنَاةُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 17]
المزيــد ...

Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 17]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Munzir ibnu A'iz ga mai tabo a fuskar nan na ƙabilar Abdulƙais kuma shugabanta - Allah Ya yarda da shi - Lallai kai kana da siffofi biyu Allah Yana sonsu, sune: Hankali, da kuma tabbata da nutsuwa da kuma rashin gaggawa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan ɗabi'antuwa da haƙuri da kuma dangana.
  2. Kwaɗaitarwa akan tabbata a cikin al'amura da kuma duba ƙarshensu.
  3. Haƙuri da dangana suna daga cikin siffofi ababen yabo.
  4. Mutum ya godewa Allah - Maɗaukakin sarki - akan abinda Ya halicce shi akansa na ɗabi'u ababen yabo.
  5. Kalmar al-Ashaj ita ce wanda aka jiwa rauni a fuska, ko a kai, ko goshi.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (35)