____
[] - []
المزيــد ...
Daga Abu Hamza Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - hadimin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [الأربعون النووية - 13]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa imani cikakke ba ya tabbata ga wani daga musulmai har sai ya so wa ɗan'uwansa abinda yake sowa kansa na ayyukan ɗa'a da nau'ukan alkairai a addini da rayuwa, kuma ya ki abinda yake ki ga kansa, idan ya ga wata tawaya ga ɗan'uwansa musulmi a addininsa, to ya yi kokari a cikin gyarata, idan ya ga wani alheri a cikinsa to ya daidaita shi ya taimake shi, ya yi masa nasiha a al'amarin Addininsa da duniyarsa.